Dun da cewa Kur”ani bai bayyana a sarari cewa hakkin saki ya kebanta da namiji ba sai dai dukkanin ayoyin da suka yi Magana kan saki suna fuskantar namiji ne kaitsaye bisa misali; ya zo a cikin wasu daga cikin ayoyi kamar haka:- {Idan kuka saki mata ...
Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
Ya zo a cikin muhimman litattafan fiqihu {hukunci} cewa mustahabbi ne a cikin tashahud na biyu karanta wannan zikiri kamar haka: {Bissimillahi wa billahi walhamdulillahi wa khairul asma' lilLah, ashhadu an la'ilaha illallah wahdahu la sharikalah, wa ash'hadu anna muhammadan abduhu wa rasuluh, arsalahu bil-haq bashiran wa ...
Tsarin tafsirin wannan zamani na da kebance - kebance da kuma da nagartar da babu ita a cikin tafsiran da suka gabata: ta bangaren amsa shibuhohi da warware tambayoyi da lamurran da suke kai- kaiwa a kasuwar tunani da kwakwalen mutane, bisa dogaro da tafarkin yin amfani da ...
Ka iya samun wani mutum yana kokarin cin mutuncin wani da yake adawa da shi ko ta hanyar bata masa rai da tsawa da tada hankali. To shi Musulunci yana ba da damar ramuwa, watau “ramuwar gayya”. Sai dai a garin ramuwar bai dace a ci mutunci ...
Adinin musulunci shi ne cikamakin addinan sama na Allah, bai kebanta ga wasu mutane kawai banda wasu ba, ko ga wani lokaci banda wani ba, sai dai shi musulunci ya zo ne ga dukkan mutane gaba daya, Kuma haka Allah (subhanahu wa ta’ala) ya so ya sanya ...
Bisa la’akari da sadanin ra’ayi da bambancin makarantu masu tsara wa mutum hanya mai fuska daya -wato karkata ga bangaren jin dadin duniya zalla da watsi da makomar mutum, Ko kuma watsi da ni’imomin Allah da dukafa ga tarbiyar ruhi shi kadai- shi ya sa addinin musulunci ya ...
Khadibul bagdadi yana cewa: Tabi’i shi ne wanda ya abokanci sahabi. Amma a cikin maganar da Hakim ya fadi akwai nuni kan saki ba kaidi kan tabi’i da cewa shi ne wanda ya hadu da sahabi kuma ya rawaito daga gare shi ko da kuwa bai abokance ...
Babgare biyu; Shi’a da Sunna duka sun ruwaito cewa hakika Zahra’a (a.s) ta fuskanci cutarwa bayan wafatin Babanta (s.a.w), da hakan ya fusatar da ita. Haka nan ya zo a ruwayoyi cewa ta yi wasiya ga Imam Amirulmuminina (a.s), da shiryata ya yi jana’izarta da daddare. Daga ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...