dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
Ayar 31 daga Surar Nur da ruwayoyi masu yawa sun kawo lamarin hijabi lullubin mata da yadda yake, yayin da Allah madaukaki yake cewa: (Surar Nur: 24: 30-31) "Ka ce wa Muminai maza da su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne ...
Hadisin Kisa’ ya zo a littafin Sahih Muslim, amma da dan wani bambanci da yadda ya zo a littattafan Shi”a, a littafin Muslim ya zo ne kamar haka: حَدَّثَنَا أَبُو بَکرِ بْنُ أَبِی شَیبَةَ، وَ مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ اللهِ بْنِ نُمَیرٍ – وَ اللَّفْظُ لِأَبِی بَکرٍ - ...
Wannan magana ko kuma muce wannan bangare bawai sabon bangare bane, asalinsa ya faro tun daga karshen rayuwar Manzo (s.a.w) inda wasu daga alamomin wadannan mutane ya bayyana, daga masu tunani kan mganar cewa “littafin Allah (s.w.t) ya ishemu riko” ta farune tun daga lokacin da Manzo ...
Bisa la'akari da tambayoyin da suka gabata amsa ta farko da ta biyu zasu kasance kamar haka ne: a- Ba a yi bayani karara ba kan batun rashin shigar malami jagora a cikin doka ba. Don haka idan irin wannan ne jagora malami zai iya ...
Tabbas Allah mai tsarki da daukaka mai hikima ne ta kowace fuska, sannan dukkanin ayyukansa ya yi su ne bisa asasi na hikima ta karshe, to doron wannan asasi dukkanin samammu Allah ya halicce su ne a bisa doron hikima ta karshe, kamar yadda ya suranta su ...
Alaka tsakanin wadanda ba muharramai ba na da fadin gaske wannan ba kokwanto a cikinsa duk da cewa wannan tambaya ba kai tsaye take nuna wace irin alka kake nufi ba maganar da ka yo na da harshen damo sai dai ba zai yiwu a amsa ta ...
Nufin Allah da iradar sa na da tsari da kaidoji (ko dokoki), kuma ayyukan sa ba mara sa ma’ana da manufa ba ne, ballantana ma bisa tsarin na hikima da ilimi da tausayi yake zaratar da komai. Don haka ne ma yake zabar wasu daidaiku daga ma’abota ...
Idan muka koma wa tarihi da littattafansa zamu ga cewa Abubakar dan Ali dan Laila ‘yar Mas’ud assakafi, da Umar dan Ali dan Ummu habib, da Usman dan Ali dan ummul Banin (s), dukkansu ‘ya’yan Imam Ali (a.s) ne, kuma bayan mun duba sanadin ambatonsu da wadannan ...
Daga cikin Jimillar Akidun Shi’a Imamiyya Isna Ashariyya, shi ne cewa su Imamai Ma’sumai (a.s) ya wajaba su zamo Tsarkakku ne daga Dukkan wasu Sharri, da Sabo. Abun da aka Ambata kuma a cikin wannan Tambayar babu wata Warwara mai Rusarwa a ciki, babu abin ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...