A bisa la’akari da bayanai masu zuwa zamu bayanin kuma mu bada amsa kan ma’anar mabiya:- Duk da cewa Shi”a na da tsokaci kan halifofi, amma ba su dauke su a matsayin wadanda suka yi ridda ba, kuma tare cewa ya zo a wasu ruwayoyi ...
Dangane da yadda ake karanta ziyarar Ashura ga wanda baya da lokacin karanta gaisuwa ko tsinuwa daya-bayan-daya, to zai iya karanta ziyarar ta wata fuska kuma ya samu ladan. An ruwaito daga Imam Hadi (a.s) ya ce: “Mai karantawa a ziyarar Ashura la’ana dari a jumla daya ...
Akwai ra’ayoyi mabanbanta masu sabani da juna dangane da karanta littatafan Dr. Ali Shari’ati. Akwai masu wuce gona da iri, akwai masu tauye shi. Sai dai daidaitaccen ra’ayi kan batun shi ne ra’ayin Sayyidul Ka’id Ali Khamana’i. Wannan shi ne ra’ayi madaidaici kuma mafi adalci a wannan ...
Bayanin da aka ambata shi wani bangare ne na hadisin kudsi da aka sani da ya zo kamar haka: “Duk wanda ya neme ni zai same ni, wnadaya same ni ya san ni, wanda kuwa ya san ni ya so ni, wanda ya so ya yi bege ...
Ma’anar marja’iyya a mahanga ta shi’anci Abu ne biyu da a ka cakuda su suka ba da ma’an bai daya wato sha’anonin (Bada fatawa) da (jibintar malamin ko shugabancinsa), Hakika malaman addini masu girma sun tsaya kyam a fagen yin bayani da shiryarwa ta hanyar bayyana hukunce-hukuncen ...
Muna da ruwayoyi da dama da suka yi magana kan ana haifar mutum ne da dacensa, ya zo a ruwayoyi cewa Allah (SW) na fadawa iblis “ban halittarwa dan Adam zuriyarsa ba face sai da na halitta maka misalinta, babu wani daya daga dan Adam face yana ...
Ana iya tabbatar da Wilaya da jagorancin ma'asumai (a.s) a cikin madogarar dalilai hudu na shari'a da ya hada da Littafi, Sunna, Hankali, Ijma'. Dukkan malaman Shi'a kalmarsu da maganarsu ta hadu gaba daya ba ma tare da koma wa maganganunsu ba, kai hatta da ...
Duk wani aiki da kan karfafa alaka tsakanin ‘yan uwa na jini, a na kiransa sada zumunci. Musulunci ya baiwa sada zumunci matukar mahimmanci sosai ta yadda ya hana katse shi ko ga kafuri ne. Sai fa in kafurin makiyi ne, mai kulle-kulle don yakar Musulunci. Idan ...
Idan muka yi duba a nutse, a kan irin lokutan da wadancan Imamai guda biyu (a.s) suka yi rayuwar su, za a fahimci dalilin da zai sa zai yi wuya a samu daman rubuta hadisansu cikin wani littafi na musamman. Amma dai wannan baya nufin cewa al’amarin ...
Mu”azu dan jabal dan amru dan ausu dan a”izu, ane masa alukunya da baban Abdurrahman, sannan ya na daga cikin mataimakan manzon Allah {s.a.w}.[1] mu”azu dan jabal tare da mutane 70 na daga cikin wadanda sukai mubaya”mar akaba sannan suka yi tarayya cikin yakoki ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...