Idan muka yi duba a nutse, a kan irin lokutan da wadancan Imamai guda biyu (a.s) suka yi rayuwar su, za a fahimci dalilin da zai sa zai yi wuya a samu daman rubuta hadisansu cikin wani littafi na musamman. Amma dai wannan baya nufin cewa al’amarin ...
Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...
Dalilin gaskata Annabawa a kowa ne zamani shi ne abin da karantarwarsu ta kunsa wadda don ita suke bayyana mu’ujizozi da kan gagari a kwaikwaya. Su wadannan mu’ujizozi suna daga cikin hujjoji bayyanannu da ke kiran mutane zuwa ga imani. Bayan haka akwai bambance-bambance na zahiri tsakanin ...
Hadisin Kisa’ ya zo a littafin Sahih Muslim, amma da dan wani bambanci da yadda ya zo a littattafan Shi”a, a littafin Muslim ya zo ne kamar haka: حَدَّثَنَا أَبُو بَکرِ بْنُ أَبِی شَیبَةَ، وَ مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ اللهِ بْنِ نُمَیرٍ – وَ اللَّفْظُ لِأَبِی بَکرٍ - ...
An yi nuni da ra’ayoyi kala-kala masu yawa a addini kuma an yi amfani da Kalmar “addini” a wurare masu yawa da ma’anoni kamar haka: 1. Duk wani imani da wani karfi boyayye na gaskiya ne ko na barna. 2-kawai addinin Allah saukakke. Don haka ...
Hakika shedan na da zuriya kuma su ma la'anannu ne kamar yadda yake la'ananne, domin su ma bisa hakika sun bi tafarkin sa kuma sun yi riko da hanyarsa da salonsa wajen batarwa da kokarin kautarwa daga tafarkin gaskiya, sun dogara da wannan hanyar a wajen batar ...
Batun Riddar sahabbai ya zo cikin ingantattun riwayoyin Ahlus sunna masu tarin yawa wasunsu ma mutawatirai ne, a daidai lokacin da riwayoyi da suka zo kan batun riddar sahabbai a littafan shi”a ba su wuce riwayoyi guda uku ba gaba daya, kamar yadda idan muka bi isdilahin ...
Bayanin da aka ambata shi wani bangare ne na hadisin kudsi da aka sani da ya zo kamar haka: “Duk wanda ya neme ni zai same ni, wnadaya same ni ya san ni, wanda kuwa ya san ni ya so ni, wanda ya so ya yi bege ...
Bama musun yiyuwar wannan ruwaya kai tsaye sai dai wannan ruwaya ba a cika samunta ba sai a litattafan da suka yi nisan zango da zamanin amirul muminin (a.s) nisanda mafi karanci shi ne shekara dubu, marubucin <Auwal musha sheen> na daga marubutan karshe ya ciro wannan ...
Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...