Musulunci ya zo ne domin ya kafa dokoki da alakar dan adamtaka. Madinar Manzon Allah (s.a.a.w) ta kasance samfuri na al’umma mai bin dokoki, ta yanda ta tsara dukkanin alakar dan Adam karkashin inuwar dokoki. A mahangar Shahid Sadar (r.a) yana cewa, musulunci ya ajiye ...
"Ashsharab" abin nufi duk abin sha "Addahiru" abin nufi mai tsaki mai tsarkakewa wannan kalma an yi amfani da ita a cikin ayoyi daban-daban a gidan aljanna ana samun abin sha mai tsarki mai dadi iri-iri mai yanayi kala-kala, hakika Kur'ani mai girma ya kawo maganar sa ...
Tabbas abin da aka gano a cikin wannan ayar ta 13 cikin Suratul Sujada mai albarka cewa Allah bai so mutane gaba dayansu su sami shiriya ba, wannan maganar ba haka ba ce, hakika abin sabanin haka ne domin Allah ya so kowa ya shiryu domin samun ...
Gwamuwar jin tsoron Allah da kaunarsa, a wasu lokutan kuma kaunarsa kawai, dangane da Allah ba wani al’amari ba ne da yake bako, domin shi ya cika dukkanin bangarorin rayuwarmu, amma saboda tsananin bayyanarsa sai mu din muka rafkana da shi. Mu sani cewa har ...
Bamu samu wannan hadisi cikin manya manyan litattafai ba kamar yadda tambaya ta nuna , saida akwai hadisai da dama da sukayi Magana mai kama da wannan cikin Litattafanmu bari mu zabi wani da yazo cikin usulul kafy yazo da takaitaccen bayani irin na mai tambaya .
Kasancewar Sayyida Fatima (a.s) ta yi shaukin ganin Salmanul Farisi hakan ba shi da wata matsala da ma’asumancinta saboda da za ka lura da farkon hadisin da ma karshensa zaka fuskanci cewa wannan haduwa da su ka yi ta kasance bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) sannan zaka ...
Lalle shi shedan daidai gwargwardon yanda ya zo a cikin Kur’ani yana da zarafin da zai iya salladuwa a kan dukkanin ‘yan Adam face bayin Allah nan da aka tsarkake. Su wadanda aka tsarkake, su ne wadannan da suka kai ga manyan–manyan mukamomi ta yanda shedan ba ...
Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na ...
Idan muka dubi tafsirin da aka kawo dangane da ayar nan mai albarka zamu iya qididdige tafsirin a cikin maganganu guda biyar, ingantacciyar maganar tana xauke da saqo wanda ya game kowa da kowa har ma da mutuntaka. Ma'anar ita ce: addini dai mas'alace ta aqida da ...
Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Kallon namiji ga jikin mace wacce ba muharrama ba haramun ne, ko da nufin ya ji dadi ko bai nufin hakan ba. Amma kallo fuska da hannaye idan ya kasance da nufin jin dadi to haramun ne, sai dai idan ya kasance ba da nufin jin dadi ...
Amsar wannan tambayar tana da bangare hudu (4): Hakikanin zunubi: Kalmar zunubi a yare tana da ma'anar laifi da sabawa, har ila yau wannan kalma tana nufin saba umarnin Ubangiji da kuskure har ma da karkacewa ko kaucewa daga dai-dai. Saboda haka, mutum mai zunubi ...