A bisa la’akari da bayanai masu zuwa zamu bayanin kuma mu bada amsa kan ma’anar mabiya:- Duk da cewa Shi”a na da tsokaci kan halifofi, amma ba su dauke su a matsayin wadanda suka yi ridda ba, kuma tare cewa ya zo a wasu ruwayoyi ...
"Ashsharab" abin nufi duk abin sha "Addahiru" abin nufi mai tsaki mai tsarkakewa wannan kalma an yi amfani da ita a cikin ayoyi daban-daban a gidan aljanna ana samun abin sha mai tsarki mai dadi iri-iri mai yanayi kala-kala, hakika Kur'ani mai girma ya kawo maganar sa ...
Lalle shi shedan daidai gwargwardon yanda ya zo a cikin Kur’ani yana da zarafin da zai iya salladuwa a kan dukkanin ‘yan Adam face bayin Allah nan da aka tsarkake. Su wadanda aka tsarkake, su ne wadannan da suka kai ga manyan–manyan mukamomi ta yanda shedan ba ...
Abin da ake nufi da Kalmar ”Rawukan da suka sauka a Farfajiyarka” su ne Shahidai, wadanda suka yi Shahada tare da Shugaban Shahidai (A.s) a Filin Karbala. Wadannan su ne Dalilan da suke Tabbatar da haka; A bisa Al’ada masu Ziyara wadanda ...
Abin da zamu kawo a dunkule shi ne msar tambayar. Hakika Kur'ani tushe ne daga tushen shari'a, kuma shi ake komawa don gane ra'ayin addini. Ba hakan nan ake istinbadi da Al-Kur'ani ba sai abubuwa biyu sun tabbata: kafa dalilin tabbatar da Al-Kur'anin, sannan ...
Dangane da tabbatar da mustahabbancin karanta kur'ani ga mamata akwai nau'in dalili kan hakan guda biyu: nau'in farko shi ne riwayoyi da suke gamammen bayani kan tunawa da mamata domin su mamata suna amfana da kyawawan ayyukanku sannan bayyanannen al'amari ne cewa karatun kur'ani yana daga cikin ...
Addinin muslunci na ganin tsarin tausayi da jin kai da tausasawa ita ce hanyar da ta fi tasiri fiye da ragowar hanyoyi, duk da cewa a wasu wurare ya zama tilas idan yaro aikata wani nau'in kuskure a ladabtar da shi ta hanyar dukansa a sakamakon aikin ...
Mutane da dama sun tafi kan cewa Imam Ali shi ne shugabansu, amma yanayin yanda suke yi masa biyayya kuma suka sallam masa ya banbanta, babu tantama tun a farko Ammar ya kasance matemaki kuma mabiyu wanda ya sallamawa imama Ali (a.s) duk da cewa ta yiyu ...
Ruwayoyi masu yawa sun nuna fifikon matsayin ilimin Imamai (a.s) a kan Annabawa, dalili kan wannan maganar shi ne kadaitakar haske da kadaitakar badinin Imamai (a.s) tare da Manzon Allah (s.a.w), saboda shi Manzon Allah (s.a.w) ya fi baki dayan Annabawa, sannan kuma ilimin Imamai an samo ...
Dun da cewa Kur”ani bai bayyana a sarari cewa hakkin saki ya kebanta da namiji ba sai dai dukkanin ayoyin da suka yi Magana kan saki suna fuskantar namiji ne kaitsaye bisa misali; ya zo a cikin wasu daga cikin ayoyi kamar haka:- {Idan kuka saki mata ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Manzo (s.a.w) ya fada cikin mustahabbai da makaruhan jima’i cikin hadisi mai tsayi, ga Imam Ali (a.s) cewa: “ … ya Ali ka da ka tara da iyalinka cikin daren babbar salla domin idan Allah yai nufinku da samun da a wannan dare zai zamo mai yatsu ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...