advanced Search
Dubawa
6108
Ranar Isar da Sako: 2012/03/04
Takaitacciyar Tambaya
Duk da kasancewar Zahara (a.s) ta bar wannan Duniyar a lokacin da take da Karancin Shekaru ne, ba ta yi tsawon Rayuwa ba, a Bangare daya ke nan, a Daya bangaren kuma Hadisan da aka karbo daga wajenta ba su da yawa, gashi ta yi shekaru goma na Yaranta, to, ta yaya za a iya suranta cewa ta kai irin wannan matsayin da irin wannan darajar? A takaice dai mene ne ya taimaka mata, Alhali tana yarinya mai shekaru goma sha takwas, ta kai matsayin da yake dai dai da na Annabawa ne, wasu irin kamala take da su har ta cancanci wannan matsayin? Don Allah a bamu amsa mai gamsarwa.
SWALI
Duk da kasancewar Zahara (a.s) ta bar wannan Duniyar a lokacin da take da Karancin Shekaru ne, ba ta yi tsawon Rayuwa ba, a Bangare daya ke nan, a Daya bangaren kuma Hadisan da aka karbo daga wajenta ba su da yawa, gashi ta yi shekaru goma na Yaranta, to, ta yaya za a iya suranta cewa ta kai irin wannan matsayin da irin wannan darajar? A takaice dai mene ne ya taimaka mata, Alhali tana yarinya mai shekaru goma sha takwas, ta kai matsayin da yake dai dai da na Annabawa ne, wasu irin kamala take da su har ta cancanci wannan matsayin? Don Allah a bamu amsa mai gamsarwa.
Amsa a Dunkule

 Ba shakka cewa Kur’ani ya bayyana a Fili cewa Annabi Isa (a.s) an ba shi Matsayi mai Girma Alhali ma yana cikin Tsumman Goyo: ’sai Ta yi nuni a gare shi sai sukace ta yaya zamu yi Magana da wanda yake cikin Tsumma, sai ya ce ni Bawan Allah ne ya bani Littafi kuma ya sanyani Annabi kuma ya sanya ni mai Albarka a duk inda nake kuma ya yi mun wasiyya da Salla da Zakka matukar ina Raye” [1]

 Haka ma a wani wuri a cikin Kur’ani zamu ga Fadar Allah Madaukaki inda ya ce: Kuma zai yi Magana da Mutane Alhali yana cikin Zanin Goyo da kuma Lokacin da yake Dattijo kuma zai zamo a cikin Salihai”[2]

 Har ma Kur’ani ya yi Bayani balo balo a game da al’amarin Annabi yahaya (a.s) a inda Allah Azza wa Jalla ya ce: ya kai Yahaya ka riki Littafin nan da Karfi kuma mun ba shi Hukunci tun Yana Dan Yaro”[3]

 Daga wadannnan Bayanan za a Fahimci cewa babu wani abin Mamaki game da samun Matsayi mai Daraja tun a Farkon Rayuwa, kai, tun A Ranakun farko ma, ko kuma a shekarun farko, kamar al ‘amarin Annabi yahaya (a.s), to, idan muka Tafiyar da wannan Ka’idar ga Shugaban Matan Halittu, wannan Maccen, Mutumiyar Allah zamu ga babu wani Rudewa ko Nisantarwa da zamu hadu da su game da samun da Sayyida Zahara ta yi ga Mukami mai daraja da daukaka, ta yanda a dalilin takawarta da tsantsenin ta samu matsayi irin na Annabawa, amma dai tabbas ita ba Annabiya ba ce, wannan matsayin babu wani mutum mai Adalci, mai girmama Kur’ani wanda ya yi imani da wajabcin jagorancin Kur’ani, da zai yi Shakkar samuwarsa gare ta.

 Ta yanda Kur’ani ya fada a fili a cikin ayar tsarkakewa cewa nufi ne na Allah, na tsarin halittar samuwa, ya nufi tsarkake Ahlul Baiti (a.s) a cikin su kuma akwai Zahara (a.s) daga barin dukkan Datti da Dauda, wanda kuma ita ce Hususiyyar Annabawa, wacce da ita ce suka samu Makami, na Annabci suka zamo Gaskatawa ne ga Fadar Allah madaukaki: Allah shi ne ya san inda zai Sanya Sakonsa”[4] sannan kuma Allah Madaukaki ya fada a cikin Littafinsa mai gima: Iyaka kawai Allah yana nufin ya Tafiyar da Dauda ne ga barin ku Ahlul Baiti kuma ya Tsarkake ku Iyakacin Tsarkakewa”[5]

 Kuma Dukkan Musulmi masu Tafsiri na dukkan Mazhabobi da Dariku sun yi Ijma’i a kan cewa wannan Aya ta Kunshi Sayyidah Zahara (a.s) to, shin akwai wani Matsayi da yake a saman wannan?

 Amma game da Abubuwan da suke Sabbaba samun irin wannan Matsayin, Wasunsu daga Mutum ne shi kansa, wasu kuma daga Tarbiyya ne, wani abun kuma wanda shi yafi Muhimmanci shi ne Ludufin Allah.

 To, amma babu lokacin kawo dukkan wadannan sharhohin a nan.

 za a iya nemansu a mahallinsu.

 Wasu binciken da suke da alaka da wannan bayanin:[6]

 • Matsayin Imaman Shi’a idan an Kwatanta da Matsayin Annabawa 9198 (lambardandalin: 9188).
 • Ma’anar Hadisin da ke cewa ba domin Fatima ba da …. 13495 (lambar dandalin: 13230).
 • Bangarori na matsayin Fatimatuz Zahara (a.s), 2837 (lambar dandalin: 3348).

 

 


[1] Maryam 29-31

[2] Ali imran 46

[3] Maryam12

[4] An’am 124

[5] Ahzab 33

[6]

 

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Yaya asalin mutum yake?
  16660 خلقت انسان
  Littattafan riwaya da na tarihi sun tabbatar cewa dan’adam wanda ke kan doron kasa bai kasance an same shi daga Habilu da Kabilu ba, shi dai an same shi daga dan Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na uku mai suna Shisu ko Hibatullah.
 • Mene ne hukuncin wasa da tsintsaye a musulunci?
  6970 نگهداری و شکار حیوانات
  Shi wasan a kan kansa ba haramun ba ne, sai dai idan yakan cutar da mutanen da ke kusa ko na nesa kamar makoci yakan samu hukunci daban kamar yadda malamai masana tunanin dan Adam suka fada cewa ya kamata gare shi ya kula sosai da irin ...
 • me ake nufi da duniyar zarra
  7352 پیمان پروردگار با مردم
  Duniyar zarra ko kuma duniyar alkawari, na nufin wani lokaci ko wata marhala ko mahalli ko kuma wata duniya ce wacce Allah ta’ala ya fitar da rayukan dukkanin mutane daga cikin tsatson Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi), a bisa kankanuwar sura sosai, kuma ...
 • Dan Da Ma’aurata Biyu Musulmi Suka Haifa, Shin Shi A Gabar Farko Shi Musulmi Ne Ko Kuma mutum Ne Kawai?
  6876 کرامت انسانی
  Mutumtakar Mutum A Tare Da Samuwar Sa Take, Ta Yanda A Dukkan Yanayi Ba Zai Yiwu A iya Raba Ta da Shi Ba, Sabanin Shi Musuluncinsa shi Ba a Danfare Da Samuwarsa yake Ba, Sai Dai Zuwa yake Yi, Wato zamu iya Suranta Samuwar Mutum Wanda Ba ...
 • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
  4703 نقش احزاب و نهادهای مدنی
  Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
 • Shin maganar cewa kowane mutum ana haifarsa da dacensa haka ne kuwa?
  5946 Dirayar Hadisi
  Muna da ruwayoyi da dama da suka yi magana kan ana haifar mutum ne da dacensa, ya zo a ruwayoyi cewa Allah (SW) na fadawa iblis “ban halittarwa dan Adam zuriyarsa ba face sai da na halitta maka misalinta, babu wani daya daga dan Adam face yana ...
 • Ku gaya mana wani hadisi game da iyakokin lullubin Mace
  8565 زن
  Ayar 31 daga Surar Nur da ruwayoyi masu yawa sun kawo lamarin hijabi lullubin mata da yadda yake, yayin da Allah madaukaki yake cewa: (Surar Nur: 24: 30-31) "Ka ce wa Muminai maza da su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne ...
 • Wadanne ne muhimman siffofin tafsirin Kur\'ani da kuma (kimarsu) matsayinsu na ilimi?
  4155 Ilimin Kur'ani
  Baba shakka kan cewa hakika sahabbai Allah Ta’ala ya kara yarda a gare su ya yarje musu sun bawa lamarin Kurani mai girma minimmanci sosai a lokacin rayuwar Manzo (s.a.w) da ma bayan wafatinsa (s.a.w) kuma sun dauki tutar addini da kyakkyawar koyarwa sama zuwa jama’a. kuma ...
 • Macece alakar dake tsakanin imamanci da tauhidi? a cikin hadisin silsila ta zinare?
  11513 ولایت، برترین عبادت
  Daga cikin abin da za a iya fahimta daga wanan ruwayar shi ne cewa, isa ga matsayin tauhidi, yana isar da mutum zuwa ga mukami na kariya da masuniyya, kuma isa ga wanan mukamin bazai yiwuba, idan ba a ketaro ta hanyar wilayah ba, madubin da ta ...
 • mi a ke nufi da zayuwar a barzahu kwana daya ko kuma kwana goma?
  9061 برزخ
  Wannan ayar na nuni da halin da mujurumai suka samu kan su bayan an busa kahon tashin kiyama suna tambayar junan su kwana nawa mu ka yi a duniyar barzahu? Mujurumai sana tunani a duniyar barzahu kwana daya ko kuma kwana goma su ka yi sai wasu ...

Mafi Dubawa