advanced Search
Dubawa
9948
Ranar Isar da Sako: 2012/03/11
Takaitacciyar Tambaya
DOMME AKE WA KA’ABA RIGA DA YADI MAI BAKIN LAUNI KAWAI?
SWALI
DOMME AKE WA KA’ABA RIGA DA YADI MAI BAKIN LAUNI KAWAI?
Amsa a Dunkule

Ana kiran wannan bakin kyalle da ake rufe Ka’aba da shi a wannan zamani da suna suturar Ka’aba ko rigar Ka’aba. A wannan zamani ne ake wa Ka’aba rika da bakin yadi, da aka yi masa zayyanar ayoyin Kur’ani da aka saka da launin ruwan gwal. Amma a zamunan baya rikar Ka’aba yadinta bai takaita da bakin launi ba, akan yi amfani da yaduka masu launi daban-daban.

Ibin Ishak yana cewa: Akan yi mata da farin yadi sannan sai a ka rika mata riga da yadi mai ratsin launuka sakar kasar Yema. Sannan a bayansa (s.a.w) Umar da Usman da Hajjaj da Ibin Zubairu su ke mata rigar da farin yadi a mata sutarar ta dibaji[1] (alhariri).

A wasu lokuta a kan yi da koren yadi da ja. A wasu lokuta akan garwaya launukan.

A farkon mulkin Nasiruddin al-Abbasi sun yi wa Ka’aban sutura mai koren launi. Amma a karshen zamanin halifancinsa sai suka yi mata da yadi mai bakin launi.

Bayan da sarakunan Masar suka kama ragama, sun yi wa Ka’aba sutura. Su kan aika sutura mai jan launi a duk shekara.[2]

A zamanin sarki Shah mai suna Sahuki sanda Iraniyawa suka albarkatu da dammar yiwa Ka’aba sutura, akan saka ne da launi mai rowan kwai. Ibin Batuta yana cewa littafin tarihin tafiye-tafiyensa: “Akan saka rikar ne da dibaji (alhariri) zalla a lardin Kurasana da ke kasar Iran, kana sai a aikata Ka’aba.

A shekaru tsakanin 1221-1229, mutanen Hijaz ne suka albarkatu da yin rigar. Su kan yi sakar ne da alhariri ja. Wadda daga baya suka musanya shi da bakin alhariri.[3]

A duk lokacin da aikin Hajji ya karato lokacin a ke canza suturar ta yadda ake fara yayeshi a hankalu kana sai ayi wa Ka’bar farar sutura. Kana bayan kare aikin Hajji sai a saka masa sabuwar suturansa.[4]

Wannan ya nuna ke nan babu wani takamaiman dalili dangane da suturar Ka’aba, sai dai ya dogare da zabin masu yin.

 


[1]. Asgarul Fa’idan, Tarikhun wa ‘Asar Makka Mukarrama wa Madina Munauwara sh 95.

[2]. Asgarul Fa’idan, Tarikhun wa ‘Asar Makka Mukarrama wa Madina Munauwara sh 96.

[3]. Sayyid Kibare Simaya Makka sh161,

[4]. Sayyid Kibare Simaya Makka sh162. Mahdi Multaji, Faharanke Danastanbahye Bish (a.s). Safare Khana Khuda, 2012 sh 97 cikin, kitabu akhbare Makka wama ja’a fiha minal ‘Asar, na Muhammad Ibin Abdullah Ibin Ahmad Azruki.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Me ye matsayi da girman da ke qarqashin xabi’u a fagagen wassanin motsa jiki?
  7762 Halayen Aiki
  Musulunci bai bar kowanne vangare daga cikin vangarorin rayuwa kara zube ba saboda kasancewarsa gamammen addini ga dukkan duniya, matuqar wannan vangaren zai taimaka ma xan Adam a yunkurinsa na samun kamalar da zata masa jagora zuwa ga rabautar duniya da lahira. Kamar yanda ya ...
 • mene ne dalilin haramcin marenan raguna?
  7219 Hikimar Hakkoki da Hukuncin Shari'a
  Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...
 • Iso in sami masaniya kan rayuwar Mikdadu dan Aswad shin zaku aiko min da halayyar rayuwarsa?
  4990 تاريخ بزرگان
  A shekata ta sha shida bayan shekarar giwa aka haifi Mikdadu dan Aswad, kuma an san shi da sunan Mikdadu dan Aswad bakinde. Kuma sunan mahaifinsa Amru kuma shi ne mutum na goma sha uku a musulunta, ta wannan janibi yana daga cikin farko- farkon musulunta kuma ...
 • Me ye alaka tsakanin Zuhudu da ci gaban zamani?
  9049 Halayen Nazari
  Kalmar zuhudu da saukin rayuwa suna daga kamalar halaye, wanda ya koma zuwa ga littattafanmu na shari'a zai samu cewa sun muhimmantar da wannan kalma da yawa, kuma sun karfafa ta sosai, suna masu nuni da kwadaitarwa da rashin damfaruwa da duniya da adonta, sai dai abin ...
 • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
  6077 زن
  Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
 • su wane ne zuri’ar yajuj da majuj? Ya karshen su ya zamo? Wane mataki Zulkarnaini ya dauka a kan su?
  16294 یأجوج و مأجوج
  Tarin ayoyi na Kur’ani da Attaura da kuma bayanan tarihi a kan yajuj na nuni da cewa wannan a’umar ta rayu ne a yankin arewacin asiya sai dai sun ta kai ma yankin kudu da yamma hare hare masu tsanani. Amma lokacin da Zulkarnaini ya yi bango ...
 • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
  15515 دلائل ولایت فقیه
  Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
 • Shin jagorancin malami sakakke ba kuwa yana nufin a yi gaban kansa a hukuma ba ne?
  4845 گستره عمل ولی فقیه
  Jagorancin malami wani isdilahi ne na fikihu da yake nuni da fagagen aiki da jagoranci da kuma wadanda suke karkashin wannan jagora, kuma babu wata iyaka a wannan fagen. Sai dai wannan ba yana nufin cewa babu kowace irin iyaka ko wasu ka'idoji a aiwatar da jagoranci ...
 • me ya sa Allah madaukaki ya bayyana mata da cewa su wasu halittune da suke girma cikin kawa?
  6875 زن
  Ayar da ta zo cikin tambaya, tana bayani ne a kan tunani da akida na kafiran jahiliya da suke cewa yaya mata ‘ya’yan Allah ne. Allah madaukaki a cikin wadannan ayoyin ya yi amfani da dalillai wadan da kafirai suka yadda da su domin ya nu na ...
 • A Wane lokaci tarihin musulunci ya fara?
  6978 تاريخ کلام
  Bayan aiko Manzon Allah (s.a.w) zuwa lokacin da iyakancin zagayen fadin daular musulunci ta kasance a iyakancin wani yanki daga kasan saudiyya a yanzu, a sakamakon karancin adadin musulmai da kuma Karancin faruwar mihimman abubuwan (da za‘a ayi amfani da su a KirKiri tarihi), kari a kan ...

Mafi Dubawa