advanced Search
Dubawa
903
Ranar Isar da Sako: 2019/06/16
Takaitacciyar Tambaya
Shin mutum mai yawan tafiya zai yi kasaru kan hanyarsa ta tafiya ko dawowa wacce ba ta kai kwana goma ba?
SWALI
mutum mai yawan tafiya zai yi kasaru an hanyarsa ta tafiyan da bai kai kwana goma ko dawowa?
Amsa a Dunkule
Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a  garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na cika sallah malamai suna da sabani kai amma ma fi karanci shi ne kwana daya cikin dukkanin kwanaki goma.
Duk da kasantuwar sana”ar ka shi ne tafiye tafiye sai dai kuma kwanakin tafiyar sun karanta to a lokacin irin wannan tafiyar kasaru za ka sallata sannan kuma ka da ka dau azumi sai dai idan gabanin azahar ba zaka isa ga garinku ba ko wajen da ka nufi zuwa har sai ka dauki tsawon kwanaki goma kafin risakarsa, to irin wannan yanayi za ka cika sallah ka kuma dau azumi.
 
Ayatollah sayyid ali kamna”i:
Idan nisa tsakanin garin da kake zaune da wajen da kake aiki ya haura kilomita 22/5 sannan kuma mafi karanci shi ne  a dukkanin sati ka na zuwa wannan waje sau daya to a irin wannan yanayi za ka cika sallah ka kuma dau azumi. [1]
 
Ayatollah nasir mukarim shirazi:
Idan ya kasance cikin kowanne wata biyu ko wata daya ka na tafiye tafiye sau uku cikin kowanne sati to a irin wannan yanani zaka cika sallah ka kuma dau azumi, idan ba haka ba to wajibi ne ka yi kasaru.[2]
 
Ayatollah sayyid Ali Sistani:
Sunan mai yawan tafiye tafiye na tabbata kan wanda ya kasance, a mafi karanci ya na tafiya sau uku cikin kowanne sati ko kuma kwananki goma cikin wata guda sannan kuma ya dau niyyar ci gaba da yin irin wannan tafiye tafiye wanda akalla za su kasance wata shida ko wata uku cikin kowacce shekara biyu da abin da ya yi sama da haka.
Sai kuma dole ne a watansa na farkon fara yin tafiya ya yi ihtiyadi wajen hada cikawa da kasaru.[3]
 
Ayatollah gulfaigani:
Idan ya kasance ya dau damara yin tafiye tafiye a kowanne sati tsawon kwanaki da ake la”akari da su kuma ya ci gaba da yin hakan to za a sanya shi cikin hukuncin mai yawan tafiye tafiye wanda zai dinga cika sallarsa.[4]
 
Ayatollah jawad tabrizi:
Idan ya kasance zai yi wana aiki tsawon watanni biyu ko sama da haka sannan nisan wajen aikin da garin da yake ya kai gwargwadon masafa ta shari”a sannan kuma mafi karanci a kowanne sati ya na kai kawo sau daya tsakanin garin da ya ke da wajen aikin sa, to a irin wannan yanayi zai cika sallah zai kuma dau azumi.[5]
 
Ayatollah Muhammad takiyu bahajat:
Mai yawan tafiye shi ne wanda mafi karanci a cikin kwanaki goma ya na kai kawo tsakanin garinsa da wajen da zai je da gwargwadon nisan masafar shari”a, da haddin da a al”adance mutane za su kidaya shi daga cikin masu yawan tafiye tafiye.[6]
 
 

[1]  An ciro daga tambaya ta 9153.
[2] Daga tambaya mai namba 16403.
[3] Taudhihul masa’il j1 shafi 704.
[4] Majma’ul masa’il j1 shafi 212.
[5] Istifta’at j2 shafi 81.
[6] Istifta’at j2 shafi 425.
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Me ya sa ake kashe mai ridda a Musulunci? Shin wannan hukuncin bai sabawa 'yanci akida ba?
  14864 بیشتر بدانیم
  Yin ridda ita ce bayyana fita daga addini, mafi yawanci tana kasancewa ne tare da bada gudum mawar wasu. Horon mai ridda baya game wanda ya fita daga addini amam ya boye hakan bai bayyana shi ba don kar mutane su sani. A bisa wannan tushen horon ...
 • A ina ne za a iya yin salla da taimama maimakon wankan janaba?
  6376 شرایط انتقال به تیمم
  Idan dai mani ya fita daga gare shi ya samu janaba, to wanka ya zama wajibi kansa. Sai dai a wurare guda bakwai ne zai iya yin taimama maimakon wanka da suka hada da[1]: Idan ya zama ba shi da ...
 • Shin ruwayar tashi daga Iran a karshen zamani abin la’akari ce (akwai kuwa)
  4962 نشانه های ظهور
  Duk litattafan Shi’a da sunna sun hadu kan cewa bayyanar imam mahdy (AF) wata saura zata share fagen zuwansa (bayyanarsa) zai zama ma’abocin bakaken tutoci a wannan saura su ne masu shimfide alamar kafin bayyanarsa.[1] hukumar iran da aka same ta ta kasu gida ...
 • Nawa ne adadin ‘ya’yan Adam da Hawwa?
  6572 پیامبران و کتابهای آسمانی
  Babu wani ra’ayi mai karfi – kamar yadda ya zo a cikin abubuwan da suka faru a tarihi masu yawa game da adadin ‘ya’yan Adam (a.s), don haka ne muka ga sabani mai yawa da ra’ayoyi mabambanta kan sunayensu da adadinsu, kuma zai yiwu a samu sabani ...
 • Mene ne Dalilin wilayar Ma'asumai (a.s)?
  7116 ولایت، برترین عبادت
  Ana iya tabbatar da Wilaya da jagorancin ma'asumai (a.s) a cikin madogarar dalilai hudu na shari'a da ya hada da Littafi, Sunna, Hankali, Ijma'. Dukkan malaman Shi'a kalmarsu da maganarsu ta hadu gaba daya ba ma tare da koma wa maganganunsu ba, kai hatta da ...
 • Shin zai yiyu a sami alaKa tsakanin Mutum da Aljani?.
  5889 ارتباط انسان با جهان
  Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
 • Shin da wacce mahanga Kur’ani ke kallon mutum? a matsayin wanda yake yin zalunci da jahilci, ko kuma halifan Allah a bayan kasa?
  5615 انسان و خلافت الاهی
  1- Kur’ani ya yi nuni a wasu ayoyi cewa mutum na da matsayi madaukaki sai dai amma a wani bangaren da mafiya yawan ayoyi yana zarginsa da tare da yi masa gargadi 2-matsayin dan Adam dan Adam na da wani abin mai ban mamaki wajan ...
 • a mahangar Kur’ani mene ne bambanci ibilis da shaidan?
  6519 ابلیس و شیطان
  A bisa ayoyin kuráni mai girma ibilis yana daya daga cikin aljanu, saboda yawan ibadar shi ya zamo daga cikin mala'iku, amma bayan Allah ya halicci Adam sai aka umarce shi da yi wa Adam sujada amma ya ki sai Allah ya nisantar dashi daga gare shi. ...
 • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
  1644 حدود، قصاص و دیات
  Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...
 • Mene ne sharuddan da ke sa wa Rana ta tsarkake kasa da gini?
  4267 بیشتر بدانیم
  Rana na daya daga masu tsarkakewa kamar yadda ya zo a fikhu, yadda rana ke tsarkake gini da kasa kuwa; ka da a samu tazara tsarkakakkiya tsakanin zahirin (doron) kasa da bayanta (cikinta) ko kuma ginin da hasken ranar zai sauka a kansa kamar iska ko wani ...

Mafi Dubawa